HARE-HAREN FILATO: OSINBAJO YA CE ZA A HUKUNTA MASU AIKATA LAIFI


Mataimakin Shugaban kasa Yemi Osibanjo, a ranar Litinin, ya ziyarci Plateau bayan hare-haren da ya haddasa salwantar rayukan jama’a.


A cikin kwanaki biyu da suka wuce, an kashe mutane fiye da 80 a jihar daga hare-haren da aka kai a wasu al'ummomi tara.
Osibanjo, wanda yake a jihar don gane wa kansa halin da ake ciki da kuma hulɗa tare da shugabannin a jihar, ya ce idan aka kama wadanda suka haddasa wannan rikic, zasu fuskanci fushin gwamnati.
Ya ce an tura sojoji ne domin kawo zaman lafiya a jihar.
"Shugaban Hukumar ‘yan sanda ta kasa, IGP Ibrahim Idris ya tura ma'aikata zuwa Plateau kuma Babban Jami'in Tsaro ya sanar da cewa za a tura Sojoji na musamman zuwa Filato.
"Sojoji na Musamman za su taimaka wajen kokarin kawo zaman lafiya a jihar," in ji shi.
Rundunar Sojoji suna gudanar da aikin tsaro na Operation Save Haven. Janar Abayomi Gabriel Olonisakin, ya ba da dama da kuma izinin ƙarin Sojoji na musamman zuwa Jihar Filato don kawo karshen wannan hare-haren.
Mataimakin Shugaban ya bayyana bakin cikin sa kwarai da gaske game da cin galabar da ake yi wa jama’a da basu jib a bas u gani ba.
A cewarsa, shugabanni ya kamata su guje wa abubuwa da zasu haifar da maganganu ko ayuka da zasu haifar da tashe-tashen hankula.
Gov Simon Lalong, a cikin nashi bayanin, ya yi ta haɗaka tare da iyalan wadanda suka rasa 'yan uwa da dukiya.
Lalong ya nuna bakin ciki sosai saboda faruwan wannan lamari, Beroms da Fulani sun sanya hannu kan yarjejeniyar kuma sunyi shawarwari game da yadda za'a zauna tare cikin lumana.
Ya gode wa Gwamnatin Tarayya don ba da agajin gaggawa kuma ya tabbatar da cewa Gwamnatin Tarayya za ta taimaka wa jihar ta dawo da zaman lafiya a jihar.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta



Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments