HARAJIN NAIRA MILIYAN 300 KACAL JIHAR GOMBE KE TARAWA A WATA
Hukumar Tara Kudaden Harajin Jihar Gombe, ta bayyana cewa jihar na tara kudaden harajin da ya kama daga naira milyan 300 zuwa milyan 500 a kowane wata.
Shugaban Hukumar, Mohammed Damji ne ya bayyana haka, a wata hira da ya yi da ‘yan jarida a Gombe, babban birnin jihar.
Ya ce hukumar ta toshe duk wata kafa ko ramun da kan janyo tawayar tara kudaden shiga.
“Gombe karamar jiha ce, idan ka kwatanta ta da wasu jihohi. Amma duk haka ina ganin mu na kokartawa batun tara kudaden haraji, domin mukan tara daga naira miliyan 300 zuwa milyan 500 a kowane wata.
Ya kuma tabbatar da cewa duk abin da aka tara ya na tafiya ne aljihun gwamnati, ba wani wuri ba.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku