GWAMNATIN NAJERIYA ZA TA RABA KUDADEN ABACHA WA TALAKAWA

Gwamnatin Tarayya za ta fara raba wa mabukata tallafin naira budu biyar daga watan Juli mai kamawa.



Za a fara ne da raba kudin a wasu jihohi 19 da aka ware. Jihohin dai sun hada da: Niger, Kogi, Ekiti, Osun, Oyo, Kwara, Cross River, Bauchi, Gombe, Jigawa, Benue, Taraba, Adamawa, Kano, Katsina, Kaduna, Plateau, Nasarawa, Anambra da kuma sansanin ‘yan gudun hijira a jihar Borno.
Za a rika bayarwa a kowane wata.
Jami’in Raba Kudaden Tallafin ta Hanyar Asusun Ajiyar Banki, Tukur Rumar ne ya bayyana haka.
Ya ce kudaden da za a raba din duk za su fito ne daga cikin dala milyan 322 da aka maido wa gwamnatin Shugaba Muhammadu Buhari da Abacha ya boye a kasashen Turai.
Idan ba a manta ba, har bayan da Buhari ya karbi kudin da Abacha ya boye a kasashen waje, ya sha cewa Abacha bai wawuri dukiyar kasa ba, mutum ne mai gaskiya da rikon amana.
Sai dai kuma ba kowane mutum daya ne za a bai wa kudin ba, gida-gida ne za a tika bai wa.
Wato kowane gida za a bai wa mutane gidan naira dubu biyar. Gwamnati ta ce gidaje 302,000 ne za su amfana a cikin jihohin 19.

MENENE RA'AYOYIN KU?
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta


Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

Comments