FURSUNONI SUN TSERE DAGA KURKUKU A MINNA


Wadansu yan bindiga sun kai hari a kurkuku a ranar Lahadi da yamma, cikin garin Minna. 

An kashe wani gandiroba da dan acaba, yayin da 'yan fursunoni suka tsere.
'Yan bindiga sun shiga cikin shinge.

A ranar Lahadi, 3 ga Yuni, 2018 da misalin karfe 8 na yamma, yan bindiga sun kai farmaki a wani gidan kurkuku wanda yake a Tunga a Minna.

Wannan ya haifar da mutuwar wani jami'in kurkuku da kuma dan acaba.

A halin yanzu, jami'an tsaro a jihar sun cafke fursunoni 7 da suka yi yunƙurin tserewa, sun sake dawo da su kurkukun.

Hukumomin gidan yari a Minna suna iya kokari don gano wadanda suka tsere.

Comments