ANFI SALLAH DA ADDU'A A KOWACCE RANA A NAJERIYA, FIYE DA SAURAN KASASHE
- Wuraren ibadu sunfi wuraren neman arziki yawa a kasashe masu tasowa
- Najeriya ce ta daya a duk duniya
A sabon bincike da aka fitar a kwanan nan, kan bibiyar jin ra'ayoyiyn jama'a kan ko suna baiwa addinai muhimmanci, ko kuwa suna ibada a kullum, kamar addu'a, sallah, ko zikiri, kasar Najeriya a duniya kaff, ita ce tazo na daya. Kasashen dai da aka bi sun karade duniyar nan, inda aka tuntubi mutane daga bangarori da yawa na fannonin rayuwa, kuma aka gyagije adadinsu har zuwa kashi dari.
Ga yadda kididdigar ta nuna, masu Sallah/Ibada a kowacce rana:
1) Najeriya: 95%
2) Iran 87%
3) Indonesiya 84%
4) India 75%
5) Brazil 61%
6) Turkey 60%
7) US 55%
8) Israel 27%
9) Canada 25%
10) Norway/Russia 18%
11) France 10%
12) Jamus 9%
13) Ingila 6%
14) Sin 1%
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku