AN SACE WA KANU DALA 11,000 A FILIN JIRGIN SAMA A RASHA
An sace wa Tsohon dan wasan Arsenal Nwankwo
Kanu dala 11,000 a filin jirgin saman Moscow a Sheremetyevo a yayin da zai je
domin ya fara wasan kwallon kafa wanda FIFA ta tsara.
Kanu, mai shekaru 41, wanda ya jagoranci tawagar kasa ta Najeriya
kuma ya taka leda a Arsenal da Inter Milan, an sace masa kudin ne bayan da ya
shiga jirgin zuwa Kaliningrad a filin saukar jiragen saman Sheremetyevo a Moscow
bayan ya sauka daga Londona ranarLahadi bisa ga rahoton da kamfanin dillancin
labarai ta shaida.
TASS ta fadi cewa 'yan sanda a Rasha sun ce sun tsare Jakunan
matafiya guda biyu wadanda ke dauke da kaya daga jirgin saman London.
"An kwashe dukiyar da aka sace, kuma ba da daɗewa ba za ‘a mayar da shi ga
mai shi," in ji kakakin 'yan sanda Irina Volk. 'Yan sanda sun tabbatar wa TASS
cewa kaya na Kanu ne.
Kanu ya taka leda a Kaliningrad a wasan sada zumunci ta musamman
na "Relive Legends" a ranar Lahadi a matsayin wani ɓangare na tawagar
FIFA akan kungiyar 'yan Rasha. Kanu ta lashe gasar ta 6-4.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku