AN KASHE DAN SANDA 1 YAYINDA RIKICI YA BARKE TSAKANIN YAN SHI'A DA YAN SANDA
An hallaka dan sanda daya har lahira a sabuwar rikici da ya
barke tsakanin yan sanda da yan kungiyar Shi'a a zanga-zangan da sukeyi kan
cigaba da tsare shugabansu, Sheik Ibrahim Zakzaky. Kakakin hukumar yan sanda a
jihar Kaduna, Muktar Aliyu, ya tabbatar da wannan labari da ya faru a yau
Alhamis, 1 ga watan Yuni 2018.
Game da cewarsa, dan sandan na tafiyarsa a kan
hanya kawai sai yyan Shi'an sukayi masa ribiti da caccaka masa wuka har lahira.
Kafin abkuwar wannan lamari, An rufe manyan hanyoyin zuwa babban kotun jihar
Kaduna da safiyar jiya Alhamis, 21 ga watan Yuni yayinda ake shirin gurfanar da
shugaban kungiyar IMN da aka fi sani da Shi’a, Sheikh Ibrahim El-Zakzaky. Yan
jaridan da suka tafi kotun basu samu daman shiga ba yayinda manyan jami’an
tsaro suka tare dukkan hanyoyi domin hana jama’a samun isa harabar kotun.
Hakazalika masu abubuwan hawa basu saman daman wucewa ba daga Kabala doki zuwa
Indepence way zuwa Waff road. Daga baya, an gaza cigaba da gurfanar saboda
rashin halartan Alkalin da ya kamata ya bayar da Shari'a a kotun. Sheikh
Ibrahim El-Zakzaky dai yana gurfana a kotu ne kan laifin tara mabiya ba bisa
doka ba, kokarin fito-na-fito da gwamnati.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku