AN KAMA MASU SAYAR DA JARIRAI
Hukumar
'yan sandan Abia ta kama wadansu masu sufurin yara da kuma sayar da yan jarirai,
ciki har da wata mace mai shekaru 17 mai suna Gift Daniel, wanda ta sayar da
dan jariri mai shekaru biyu bisa kimanin kudi N670,000.
Kwamishinan 'yan sandan,
Mista Anthony Ogbizi, ya bayyana hakan a ranar Litinin, yayin da yake jawabi ga
manema labaru a Umuahia akan ayyukan da aka yi.
Ogbizi ya bayyana cewa, tuni
hukumar ta yi nasarar cafke mutane guda 22, acikin su har da masu aikata wadansu
lafuka masu halaka da wannan a yayin da hukumomin tsaron suke farautar masu
aikata manyan laifuka.
A cikin hira da manema
labaru, Gift Daniel ta ce an tilasta ne ta sayar da jaririn saboda matsalar
rashin kudi.
Ta ce cewa jaririnta na
farko MA, mahaifiyarta ce ta sar da shi shi, saboda haka ta yanke shawarar
sayar da jariri na biyu.
Gift Daniel ta ce matar
da take yin fataucin yara, mai shekaru 38 mai suna Ngozi Nwaiwu ta bata Naira
dubu 50 ne, yayin da jami’an jinya da ingozoma, Kate Charles, wanda ta taimaka
mata a lokacin haifuwa, ta sami Naira dubu 30.
Har ila yau, 'yan sanda
sun kama mai suna Blessing Chukwu, mai shekaru 22, wanda ya sayar da jaririn ta,
mai sati uku da haifuwa, tare da mai saya Chinasa Okpara, mai shekaru 40.
Sauran wadanda aka kama
bisa zargin su da aikata irin wadannan laifi sun hada da Mrs Puphemia Omende da
mijinta, Kelechi, wanda shi ma likita ne.
'Yan sanda sun yi zargin
cewa ma'auratan sun taimaka wa ma'amala a gidajen su, Winnies Hospital, Okigwe,
inda aka haifi jariri.
Okpara ta ce ta sayi
jaririn a bisa Naira Dubu Dari uku da sittin (N360,000) sakamakon rashin
haifuwar ta na sama da shekaru 13.
An kama su a asibitin
Tarayya, Umuahia, an haifi jaririn ne a cikin makonni uku da suka gabata.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku