AN FITAR DA SUNAYEN WADANDA SUKA SAMI NASARAR SHIGA AIKIN DAN SANDA
Mun samu rahoton cewa, hukumar 'yan sanda ta
Najeriya ta saki jerin sunayen wadanda suka taki nasara wajen daukar su aiki na
hukumar a shekarar 2018 bayan ta gudanar da tantancewa a matakai daban-daban.
A ranar yau ta Juma'a hukumar ta wallafa jerin
sunayen mutane da suka taki nasara ta samun damar daukar su wannan aiki na
jami'an tsaro.
Abayomi Shogunle, ya bayyana a shafin sa na
dandalin sada zumuntar tuwita jerin sunayen Mutanen da suka yi nasara ta daukar
su aiki.
Babban Jami'i Abayomi ya nemi al'ummar Kasar
nan da suke nemi shiga aikin na 'yan sanda akan su duba sunayen su da ranar da
za a fara horas da su a shafin hukumar kamar
haka;
Hukumar ta kayyade
ranar 08/06/2018 a matsayin ranar fara karbar horo, inda ta bayar da talala har
zuwa ranar 13/06/2018. Ta kuma yi gargadin duk wanda ya wuce wannan rana to ya
yi asarar aikin sa. Rahotanni sun bayyana cewa, wannan daukar aiki na hukumar
'yan sanda ya biyo bayan umarnin Shugaban Kasa Muhammadu Buhari na daukar
sabbin jami'ai 6, 000 a fadin Kasar nan.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku