ABUBUWAN DA REFEREE YA FADAWA MIKEL OBI JIYA BAYAN AN TASHI WASA


Kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Super Eagles, John Obi Mikel yace ya kamata ace an baiwa 'yan kwallon Najeriya damar daukan Penalty wanda dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Argentina yayi. Tsohon tauraron kungiyar kwallon kafa ta Chelsea yace baiga dalilin da ya hana a ba Najeriya damar penalty ba bayan Marcos Rojo ya taba kwallon da hannun shi kuma kowa ya gani.



Argentina taci wasan, wanda zai bata damar kaiwa ga zango na gaba, inda zata fuskanci kasar Faransa. Kaftin din Super Eagles, John Obi yace yakamata rafalin da ya shugabanci wasan tsakanin Najeriya da Argentina, Cuneyt Cakir, ya basu damar penalty. Najeriya dai ta fita daga gasar kwallon kafa ta duniya na shekarar 2018 bayan da kasar Argentina ta lashe wasan jiya da ci2 da 1. A lokacin da ake kunnen doki tsakanin Najeriya da Argentina, kwallon ta bigi hannun Marcos Rojo, dalilin da yasa a baiwa Najeriya damar daukan penalty din kenan, inda shi kuma rafalin yace a cigaba da wasa, wanda ya kawo cece-ku-ce daga yan wasan Najeriya. John Obi Mikel yace rafalin ya bayyana mishi dalilin hanasu Penalty, inda yace "Idan ka kalli wasan Portugal jiya, wannan bai yi ko kusa da wancan ba. Wannan yafi wancan muni. Mun kuma gani.
Da Mikel ya tambaye shi mai ya hana a basu penalty din? Sai rafalin yace shima bai sani ba.

Comments