SOJOJIN SAMAN NAJERIYA NAF TA HALLAKA YAN KUNGIYAR BOKO HARAM A BAMA

Sojin saman Najeriya (NAF) ta ce ta hallaka 'yan ta'addan Boko Haram ta wurin amfani da jiragen yaki, a Arewa maso gabashin kasar.
Babban Daraktan Harkokin Jakadancin NAF, AVM.Olatokunbo Adesanya, wanda ya tabbatar da hakan a wata sanarwa ran Jumma'a a babban birnin tarayya Abuja, ya ce an kai farmakin ne tare da amfani da jiragen yakin a ran talata.
"A cikin rana ta biyu da suka fara aiki gadangadan, " Thunder Strike ", wanda wata bangare ne na Operation Lafiya Dole (ATF) ta gudanar da bincike game da yan ta'addancin Boko Haram (BHT) a arewa maso gabacin kasar.

Comments