MUTANE DA YAWA SUN MUTU SAKAMAKON FASHEWAR BAM A MUBI, JIHAR ADAMAWA


Mutane da yawa sun razana, ranar 1 ga watan Mayu, sakamakon fashewar Bam din da ya janyo mutuwar wadansu mutane a garin Mubi, Jihar Adamawa a arewa maso gabashin Najeriya, rahoton da kamfanin dillancin labarai na (NAN) ta bayar ta yake tabbatar da wannan lamarin, shugaban kungiyar Mubi ta Arewa, Alhaji Musa Bello, ya ce an kai hare-haren ne da misalin karfe 3:00 na yamma. Ya ce: "Abin da zan iya fada maka yanzu shi ne cewa ina kan hanyar zuwa wurin don taimakawa wajen fitar da wadanda suka mutu. Babu wanda zai iya gaya maku yawan wadanda suka mutu da wadanda suka jikkata a halin yanzu. "

sakataren hukumar kula da gaggawa ta jihar, Haruna Furo ya nuna tashin hankalinsa amma ya ce babu cikakkun bayanai a yanzu. Wani mazaunin Mubi, wanda ake kira Buba, ya ce fashewar ta faru a masallaci da kasuwar kayan tufafi na biyu.


Comments