KUNGIYAR TSEGUN NIGER DELTA TA BA WA GWAMNATI KWANAKI 14 KO TA FARA BARIN ALA-TSINE
Wata kungiyar tsagerun Niger Delta ta bawa gwamnantin tarayya wa’adin kwanaki 14 ta tabbata ta samar da isassun kudaden da jami’ar tarayya ta nazarin albarkatun man fetir (Petroleum Resources, (FUPRE), Effurun), dake jihar Delta, a cikin kasafin kudi na 2018. Tsagerun dai sun bayar da wa’adin na sati biyu ga gwamnati tarayya ko kuma ta fuskanci fushinsu. A wani jawabi da shugabannin sashin aiyuka (Janar) Orubu Ekpe da kuma na sashin tsaro (Janar) Mike Agbalele suka rattaba hannu, sun ce, “suna gargadin gwamnatin da ta tabbata da ware isassun kudi ga jami’ar a cikin kasafin kudin bana ko kuma su zari makamansu su koma aikin fasa bututun mai da kamar yadda suka saba. A cewarsu, ana sane aka ki ware kudin da jami’ar take bukata a cikin kasafin 2018 da shugaba Muhammadu Buhari ya mikawa majalisa domin sahalewa. A cewarsu, “An warewa ma’aikatar kula da yankin Arewa maso gabas (NEDC) N45b, duk kuwa da cewa an riga amincewa da daftarin dokar jami’ar ta FUPRE kafin amicewa da daftarin kafa hukumar ta NEDC.”
Kungiyar tsageru ta kuma yabawa Shugaba Buhari bisa amincewa da daftarin dokar kafa jami’ar ta FUPRE da kuma fara aikin jami’ar Nigerian Maritime University dake jihar Delta. Amma sai dai suna bukatar shugaba Buharin da ya amincewa majalisa ta sakarwa wannan jamia’a da suke burin ganin ta kafa kudade musamman duba da tashin farashin danyan mai a kasuwar duniya daga $45 zuwa $72, wanda hakan ya haifar da samun rarar kudade masu nauyi har biliyan N152b. A cewarsu. Kungiyar tsagerun ta ULF ta ce, ta samu wasu bayai da suke nuni da rashin ware kudi ga jami’ar a cikin kasafin kudi na 2018 wata makarkashiya ce don mayarda jami’ar Arewacin Najeriya, kuma kar suke kallon duk wani tuggu da ake yin a mayar da yankin baya na Niger Delta baya.
A cewar kungiyar, an bawa makarantu kamar irinsu National Institute of Petroleum, Policy and Strategic (NIPPS) da kuma National College of Petroleum, Kaduna Naira N25b duk kuwa da cewa basu fara aiki ba, yayinda jami’ar FUPRE da ta shafe kimanin shekaru 11 ba ta taba samun sisi daga Ma'aikatar albarkatun man fetir ta kasa (PTDF). A saboda haka tsegerun su kayi kira ga dukkan ilahirin sauran kungiyoyin tsagerun yankin da su mara musu baya wajen fafutukar kwatowa yankin nasu yanci. kuma wannan karon in suka fara ba za su ci maganar kowa ta batun sulhu ko tsagaita wuta ba, sannan suka gargadi duk kamfanonin hakar mai na yankin da su shirya.

Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku