KASHI ƊAYA DAGA CIKIN UKU NA YAN NIJERIYA NA FAMA DA MATSALAR HAWAN JINI
Kungiyar Harkokin masu hawan jinni na kasa (NHS) ta ce kashi
daya daga cikin uku na yawan jama'ar Nijeriya suna da matsanancin matsalar
Hawan jinni.
Shugaban kungiyar, Farfesa Ayodele Omotoso, ya bayyana wannan a
cikin wata sanarwa da aka bayar a ranar Alhamis, don tunawa da Ranar masu fama
da hawan jini
Omotoso, wanda yake aiki a sashen kula da cututtukar zuciya a Asibitin Jami'ar Magunguna da ke garin (UITH),
ya ce KAN MAGANA na 2018 World Radiation Day shi ne: "Ku san
lambobinku".
"Ma'anar KAN MAGANA na 2018 shine " kowa ya san lambar
hawan jinin sa".
Kwararren likitan ya ce kashi daya bisa uku na 'yan Najeriya ne
sukan je asibiti don sanin yanayin hawa ko saukan jinin su, yayin da kashi daya
kuma suke shan magunguna da zasu saukaka hawan jinin tasu.
Ya bayyana cewa makasudin wannan rana na masu hawan jinni itace
domin fadakar da al’umma kan hatsari da ke tattare da hawan jini da kuma yadda
za’a kiyaye abubuwan da zasu janyo hatsari ga lafiyan zuciyar mutum.
"Abin da ta fi dacewa ita ce ta ƙarfafa al’umma su rika
zuwa asibiti domin sanin ko jinin su ta hau ko ta sauka," inji Omotoso.
Shugaban NHS ya shawarci mutane su guje wa yin amfani da gishiri
mai yawa kuma su ci abinci mai kyau tare da amfani da 'ya'yan itatuwa da kayan
marmari na yau da kullum.
Ya shawarci kowa da kowa ya yi ƙoƙari ya yi amfani da akalla
minti 30 na aikin yau da kullum da kuma rage nauyin su.
"Ku guje wa dabi’a mara kyau kamar shan taba da shan giya
ko kayan barasa," inji Omotoso.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku