JAM'IYYAR PDP TA SANYA DANKWANBO A MATSAYIN DAN TAKARAR SHUGABAN KASA 2019:


Koda yake har yanzu bai sanar da manufarsa na yin takara da Shugaba Muhammadu Buhari ba, na Jam'iyyar APC, kungiyoyi daban-daban da kuma tarurrukan siyasa a Jam'iyyar PDP, su na kokarin su tsayar da Gwamna Ibrahim Hassan Dankwanbo, na Jihar Gombe.




" Wadansu tsofaffin gwamnoni da wadanda suke kan karagar mulki, har ma da manyan ‘yan jam’iyar PDP, da wadansu ministoci da masu rike da manyan mukamai na gwamnati sun bayyana Gwamna Ibrahim Hasan Dankwambo a matsayin fitacce wanda ya dace a tsayar domin ganin irin rawan da ya taka a cikin shekaru bakwai da suka gabata a mulkin da yayi a jihar Gombe.
Dankwanbo shi ne Babban Akanta janar na kasa kafin ya yi nasarar lashe  zaben gwamnan Jihar Gombe a shekara ta 2011. An yi la'akari  ne da cewa yayi nasarar Sake fuskar jihar sa da kananan albarkatu na jihar. An kuma bayyana shi a matsayin mai gaskiya da rikon amana.
Har ila yau, a tseren wa'adin takarar shugabancin kasar nan karkashin jam’iyar PDP, tsohon Mataimakin Shugaban kasa, Atiku Abubakar da tsohon Gwamnan Jihar Jigawa, Sule Lamido suke neman TIKET na takarar shugabancin kasar Najeriya.
Dankwambo, mai shekaru 56, an haife shi a ranar 4 ga Afrilun 1962 a Herwagana Ward a Gombe, Jihar Gombe. Ya halarci makarantar firamare a Central Primary School na Gombe da makarantar sakandaren gwamnati (GSS Billiri) a jihar Gombe. Ya tafi Jami'ar Ahmadu Bello a Zaria kuma ya kammala karatun digiri tare da digiri na digiri na ilimin lissafi.

Comments