CUTAR EBOLA TA YADU ZUWA WASU MANYAN BIRANEN CONGO
Ministan
kiwon lafiyar kasar Congo ya ce cutar Ebola ta yadu zuwa babban birnin kasar
Equateur, batun da ya jawa tashin hankali a kasar baki daya.
Ministan kiwon lafiya, Oly Ilunga, ya ce mutane biyu da ake zaton sun kamu da cutar zazzabin sun ruwaito wa yankunan kiwon lafiya na Wangata, wanda ya hada da garin Mbandaka, kimanin kilomita 150 (93 mil) daga Pleasero, wata karkara inda aka samu barkewan cutar.
Yace wani samfurin ya
tabbatar da cutar Ebola, ya kawo adadin marasa lafiya a yankuna uku.
Ilunga ya ce kasar Congo
tana fuskantar barazana da kuma babban hatsari, sakamakon yaduwar cutar. Ya ce masana ilmin lissafi suna aiki tukuru don
gano adadin yawan wadanda suka kamu da cutar, ciki har da mutane 500 da aka
gano.
Kasar Congo ta bayar da
rahoton cewa mutane 23 ne cikin 42 da suka rasa ransu sakamakon barkewan cutar
a cikin kasar.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku