AN KASHE MANAJAN KAMFANIN DANGOTE

Wadansu yan bindiga sun harbe Manajan Kamfanin Simintin Dangote, Deep Kamra, mai kula da kamfanin Dangote Industries Limited a Habasha, ya mutu a ranar Laraba bayan da yan bindigar suka tare shi a yankin Oromiya lokacin da yake hanyar san a komawa gida, Addis Ababa bayan tashin sa daga ma'aikata.

Bayan kashe shi da suka yi, sai suka harbe sakatare da kuma direban Manajan Kamfanin har lahira.


Comments