AN KAMA WATA 'YAR KUNAN BAKIN WAKE A GASHUA

Sojojin Najeriya sun ce wasu fararen hula masu karfin hali a ranar Lahadi sun yi yunkurin cafke wata mata yar kunan bakin wake tattare da bam da zata tayar a wani masallaci  da da ke garin Gashua na Gujba , a garin Yobe.

Col. Onyema Nwachukwu, jami'in hulda da jama'a, na operation Lafiya Dole, ya bayyana wannan, a cikin wata sanarwa da aka bayar, a Maiduguri.

"An kama ta a lokacin da 'yan garin suka gano cewa tana dauke da bamabamai, nan take sai  aka mika ta ga dakaru a Azare.

Comments