YAN KUNAN BAKIN WAKE SUN TADA BOM A GARIN MAIDUGURI
AN KASHE MUTANE HUDU A HARIN KUNAN BAKIN WAKE DA AKA KAI A MAIDUGURI.
Maiduguri (Nijeriya) (AFP) - Akalla mutane hudu ne aka kashe yayin da 'yan ta'addan Boko Haram suka kai farmaki a babban birni na arewa maso gabashin Nijeriya,
Rikicin ya rikitar da garin Maiduguri a ranar Alhamis, tare da nuna alamun cewa masu jihadi suna ƙoƙari su isa Barikin Soji da aka fi sani da Giwa Barak.
A garin Maiduguri, Bashir Garga, daga hukumar kula da gaggawa ta kasa ta ce: "Akwai mutane hudu wadanda suka sheka lahira sakamakon wannan hari yayin da wadansu da yawa kuma sun sami rauni.
Wasu 'yan bindiga guda biyar sun mutu a yayin da suke yunkurin tada bom.
"An fitar da wadanda aka jikkata da gawawwaki zuwa asibiti a Maiduguri, a jihar Borno," in ji shugaban 'yan sandan Damian Chukwu.
Rikicin da aka yi jiya Alhamis, ya yi sauki ne bayan da rundunan soji suka nuna bajintar su tare da taimakon sojojin sama.
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku