BAYAN NASARAR ATIKU ABUBAKAR, ME JAMA'A SUKE CEWA?

Dazu ne dai labari ya isa Duniya cewa tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar ya lashe zaben fitar da gwani na Jam’iyyar PDP inda zai yi takarar Shugaban kasa da Muhammadu Buhari a zaben 2019. 



Mun kawo kadan daga cikin manyan bayanin da wasu masu bibiyar siyasa a kasar su ke yi. Ga kadan daga ciki: 

Ina taya Atiku murnar wannan nasara na samun tikitin PDP domin takarar badi. Na jinjinawa irin wannan namijin kokari da jajircewa na Atiku a fagen siyasa inda ya fara kafa sunan sa tun shekaru 25 da su ka wuce a lokacin Marigayi MKO Abiola. 
-
Inji Dele Momodu 


Wani Ya Ce:
Atiku ya nuna Gwamna Wike cewa akwai banbancin wanda ya koyi siyasa wajen Shehu Yaradua da kuma masu yi wa Abokan adawar su barazana a gaban Talabijin Duniya. 
- Japheth Omojuwa 


A 2019 dai za a kara ne tsakanin Muhammadu Buhari mai shekaru 76 da kuma Atiku Abubakar mai shekaru 72 a Duniya. Ko wanene na zaba tsakanin su.
Ebuka Uchendu 


Wani Masoyin Rabiu Musa Kwankwaso kuwa cewa yayi: 

Wata guda da su ka wuce na ji Dr. Hakeem Baba-Ahmed yana cewa manyan ‘Yan takaran Shugaban kasa da su ka fi karfi a PDP mutum 3 ne; Aminu Tambuwal, Bukola Saraki da Atiku Abubakar. Yanzu kam na fahimci gaskiya. 
-  Abubakar Dadiyata 

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments