AN KAMA MUTANE 22 DA KE DA HANNU A RIKICIN KADUNA


- Hukumar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane 22 da ta ke zargin na da alaka ta kai tsaye da kisan mutane a rikicin Kaduna 
- Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai 
- Kazalika ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin wadanda su ka rasa 'yan uwansu sanadiyar rikicin 

Hukumar 'yan sandan Najeriya ta cafke wasu mutane 22 da ta ke zargin na da alaka ta kai tsaye da kisan mutane a kasuwar Magani da ke karamar hukumar Kajuru a jihar Kaduna. Kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, Jimoh Moshood, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawa da manema labarai yau, a Abuja. 

"Mun kama mutane 22 da ke da alaka ta kai tsaye da kisan jama'a, su na ajiye wurin mu kuma su na taimakawa jami'anmu da muhimman bayanai a kan rikicin," a cewar Moshood. 



Jimoh Moshood Source: Twitter 


Moshood ya kara da cewar yanzu haka zaman lafiya ya dawo tare da bayyana cewar an sako wasu manyan mutane da aka sace yayin rikicin. 

Kazalika ya mika sakon ta'aziyya ga iyalin wadanda su ka rasa 'yan uwansu sanadiyar rikicin. 

"Shugaban rundunar 'yan sanda na kasa, Ibrahim Idris, ya yi Alla-wadai da afkuwar rikicin. Sannan ya kafa wani kwamitin bincike na musamman da zai gudanar da bincike a kan kisan jama'ar da ba su aikata laifin komai ba," kamar yadda Moshood ya fada. 

Comments