Monday, September 17, 2018

ZIYARAR THERESA MAY BA YA YANA NUFIN TSAYAR DA BUHARI BANE – HUKUMAR BIRTANIA


Babban hukumar kasar Birtaniya a Najeriya tace ziyarar da Theresa May, Fiaye Ministar Birtaniya ta kawo kwanan nan, ba yana nufin tsayar da Shugaban kasa Muhammadu Buhari kowani dan takara bane.


Laura Beaufils, mataimakiyar kwamishinan Birtaniya a Najeriya, ta bayyana hakan a jawabin da tayi a wani taron tattauanwa da hukumar ta shiryawa yan jarida a Lagas a ranar Juma’a. Ta kuma bayyana jajircewar gwamanatin Birtaniya wajen kashe Euro miliyan 47.4 a shirin zurfafa damokradiyya a Najeriya.


Da take Magana a kan rawar ganin da Birtaniya ke takawa wajen zurfafa damokradiyyar Najeriya, Beaufils ta bayyana cewa gwamnatin Birtaniya bata da kudirin sanya hannu a sakamakon zaben 2019, ta kara da cewa babu wani dan takara da tafi so.


Gwamnan jihar Gombe kuma dan takarar shugaban kasa a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party’s (PDP), Ibrahim Dankwambo ya nuna jajircewarsa na son kawo karshen duk wani kashe-kashe na kabilanci da addini a fadin kasar, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa a zaben 2019. Dankwambo ya bayyana hakan a wata sanarwa da sanya hannun Dr Ayoade Adewopo, daraktan labarai na kungiyar kamfen dinsa a Abuja a ranar Litinin, 17 ga watan Satumba.



 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  

No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku