ZAMU KASHE LEAH SHARIBU NAN DA WATA GUDA – BOKO HARAM SUNYI BARAZANA GA GWAMNATIN TARAYYA


Kungiyar yan ta’addan Boko Haram sun yi barazanar kashe Leah Sharibu, yan makarantar Dapci dake jihar Yobe guda daya tilo da ta saura a hannunsu cikin 119 da aka sace a watan Fabrairu.


Barazanar na zuwa ne yayinda gamayyar kungiyar Boko Haram suka kashe Saifura Ahmed, daya daga cikin ma’aikatan agaji uku da aka sace a Rann, karamar hukumar Kala Balge.

 A cewar shafin The Cable, an sace Ahmed ne a lokaci wata mamaya da aka kai sansanin soji a yankin a ranar 1 ga watan Maris. Akalla sojoji hudu, jami’an yan sanda da ma’aikatan hukumar agaji uku aka kashe a harin.

Hauwa Leman, daya daga cikin ma’aikatan da aka sace ta aikawa daya daga cikin kawayenta sakon murya ida ta bukaci ta fadama iyayenta cewar an kamata.

Yan ta’addan sun yi ikirarin cewa sun tuntubi gwamnati akan kamunamma babu wani bayani. “Mun tuntubi gwamnati ta hanyar rubutu sannan kuma mun aike da sakonin murya amma gwamnati tayi watsi damu. Don haka ga sakon jini,” inji kakakin kungiyar wanda bai bayyana sunansa ba. “Sauran malamar jinya da mai karban haihuwa da zamu hukunta kamar haka a wata daya mai zuwa, harda Leah Sharibu.”





 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  

Comments