TSOHON KOCIN REAL MADRID ZIDANE YA GINDAYAWA MAN UTD SHARUDAN KARBAR AIKIN MOURINHO



Tsohon Kocin Real Madrid Zinedine Zidane ya lissafowa Kungiyar Manchester United sharudan sa idan har ta so ya dawi horas da ‘Yan wasan ta inda ya kawo jerin ‘Yan wasan da yake so a saya masa.

Babban Kocin ‘Dan kasar Faransa Zidane ya fadawa Kungiyar Manchester United cewa sai an kashe masa makudan kudi har fam Miliyan 300 na Euro idan zai canji Jose Mourinho a Kulob din. ‘Yan wasan da Zidane yake so sun hada da:

1. Edison Cavani Zidane zai so ya ga ‘Dan wasan gaba Edison Cavani a Kulob din kafin ya karbi aikin horas da United. Yanzu haka dai an fara tunani cewa Jose Mourimho ba zai kai labari ba a Kungiyar.

2. Toni Kroos Haka kuma tsohon Kocin na Real Madrid zai nemi a sayo masa wani tsohon ‘Dan wasan tsakiyar sa Toni Kroos idan har ana so a gan sa a Manchester. A baya Manchester ta nemi Kroos.

3. Thiago Alcantra Har wa yau, babban Kocin zai so Manchester ta sayo masa tsohon ‘Dan wasan Barcelona. Shi ma dai Alcantar ‘Dan wasan tsakiya ne da yake bugawa Bayern Munich da Sifen wasa.

4. James Rodriguez Zinedine Zidane zai kuma so ya ga an ajiye masa James Rodeiguez a kulob din idan har da gaske ana neman ya canji Mourinho. Zidane ne dai ya ba Bayern Munich aron James lokacin yana Real.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments