SHUGABA BUHARI YA DAWO DAGA KASAR SIN


Laale marhabun; shugaba Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya da daren jiya Alhamis, 6 ga watan Satumba 2018 bayan share kwanaki shida a kasar Sin inda ya halarci taron hadin kan kasar Sin da nahiyar Afrika wato FOCAC tare da wasu shugabannin kasashen Afrika.



Shugaba Buhari ya tafi kasar Sin ranan Juma'a, 31 ga watan Agusta 2018 bayan karban bakuncin shugabar kasar Jamus, Angela Merkel, a fadar shugaban kasa, Aso Villa. An gudanar da wannan taro ne karo na bakwai a wannan mako a kasar Sin inda shugabannin kasashen Afrika daban-daban suka halarta.

Shugaba Buhari ya gabatar da jawabi a wannan taro inda ya bayyana alfanun da Najeriya ta samu a hadin kan da take yi da kasar Sin. Kana ya karyata rahotannin cewa Najeriya ba tada kudin biyan basussukan da take karba daga hannun gwamnatin kasar.
Daga cikin tsarabar da Buhari dawo da su, akwai alkawarin gina masana'antu, layin dogo, da sanya hannun jari a jihohi daban-daban.

A ranan Laraba, shugaba Muhammadu Buhari ya gana da shugabannin kamfanin ‘Ruyi Group, wata babbar kamfanin a kasar Sin inda suka tattauna kan irin hannun jarin da za su sanya a Najeriya. Bayan ganawar, kamfanin ta alanta cewa za ta sanya hannun jarin dala miliyan dari biyu ($200m) wajen gina tashar mota a jihar Kano, gonan auduga a jihar Katsina, da masaka a jihar Abiya da Legas.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com


Comments