HUKUMAR 'YAN SANDA TA NAJERIYA TA HANA KARIN GIRMA GA MASU KATON TUMBI

Hukumar Kula da ‘Yan kasa ta Najeriya ta koka yadda akasarin ‘yan sandan kasar ake samunsu da katon tumbi saboda rashin motsa jiki.

Daga yanzu Hukumar ta ce duk wani dan sanda mai katon tumbi to kuwa shi da samun Karin girma saidai ya hangi wasu an yi masu.
Majiyar Naij.com ta ce a cikin Wata sanarwa daga Hukumar na cewa bayaga neman kowa ya rage girman tumbinsa dole ne masu bukatan samun Karin girma su yi nasarar cin jarabawa da ake yi masu. 
Sanarwar na cewa Shugaban Hukumar  kula da 'yan sanda Musliu Smith ya damu matuka da yadda ake yawaitan sauyawa wasu ‘yan sanda wuraren aiki maimakon a bar mutun ya yi akalla shekaru biyu zuwa uku.




 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  

Comments