DANDALIN KANNYWOOD: GASKIYAR ALAKA TA DA ADAM A. ZANGO - ZAINAB INDOMIE



- Zainab Indomie ta fadi me ke tsakanin ta da Adam Zango
- Tace ya taimake ta sosai
- Tace ta dauke shi a matsayin dan uwa



Fitacciyar jarumar nan ta fina-finan Hausa a masana'antar Kannywood watau Zainab Abdullahi da aka fi sani da Zainab Indomie ta bayyana ainihin alakar ta da jarumi, Adam A. Zango.
Jarumar dai wadda yanzu haka ta sanar da dawowar ta harkokin fina-finai ta ce ita ta dauki Adamu a matsayin ubangida a gare ta da har zata iya kiran sa dan uwa amma babu zancen soyayya a tsakanin su. Zainab Indomie ta kara da cewa: "Zango ya na taimaka min sosai, musamman don ganin na cimma nasara a wannan sana'a".

wannan dai na zuwa ne a lokacin da ake ta rade-raden cewa jaruman suna shirin yin aure ne sakamakon soyayyar dake tsakanin su musamman ma bayan da Adam Zango din ya saki matar sa. Ita dai Zainab Indomie, kamar yadda masoyanta da ma'abota fina-finan Hausa suka fi sanin ta, ta yi fice a masana'antar Kannywood a shekarun baya musamman sakamakon irin rawar da ta taka a wasu manyan fina-finai. Daga cikin fina-finan da suka sanya jarumar ta shahara akwai 'Wali-Jam', da 'Ali' da 'Garinmu Da Zafi' da sauransu.



 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  

Comments