AN RANTSAR DA IBRAHIM BOUBACAR KEITA A BAMAKO


An rantsar da shugaban kasar Mali Ibrahim Boubacar Keita domin yin wa’adi na biyu sakamakon nasarar da ya samu a zaben da ya gabata a Bamako.

Zababben shugaban ya sha alwashin tabbatar da tsaro da zaman lafiya a cikin kasar, a matsayin babban abinda zai sanya a gaba.
Sai dai yayin da ake gudanar da rantsuwar yan tawaye sun kai hari garin Menaka, inda suka raunana sojin Majalisar Dinkin Duniya dake aikin samar da zaman lafiya guda.


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  




Comments