Tuesday, September 4, 2018

2019: DAVID MARK DALILIN DA YASA YA KE SON ZAMA SHUGABAN KASA


- Sanata David Mark ya shiga sahun masu neman tikitin takarar shugabancin kasa a jam'iyyar PDP
- David Mark ya ce daya daga cikin abinda da yasa ya ke son zama shugaban kasa shine canja fasalin Najeriya
- Ya kuma lissafo wasu muhimman dalilai a karkashin tsarinsa na musamman mai taken '730'
Tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Marki ya bayyana dalilan da yasa ya shiga sahun masu neman takarar zama shugaban kasa a Najeriya. David Marki, wanda ke waliktan mazabar Kudancin Benue, ya siya tikitin takararsa ne a sakatariyar jam'iyyar PDP da ke Abuja a yau Talata. Dan majalisar da yafi kowa dade wa a majalisar ya lissafo wasu dalilai da ya sanya shi shiga takarar shugabancin kasar a karkashin inuwar jam'iyyar PDP.
"Duk da irin banbance-banbancen siyasarmu, babu shaka lokaci ya yi da ya kamata a fuskanci batun sake fasalin Najeriya," kamar yadda David Mark ya fadi a wata sako mai dauke da sa hannun mai taimaka masa a fannin yada labarai.

"Nayi imanin cewa sake fasalin zai karfafa zumunci tsakaninmu da hadin kai saboda babu wanda zai rika ganin kamar an mayar da shi saniyan ware kuma mutane za su iya zama a kowanne yanki a kasar ba tare da fargaba ko cin fuska ba." Inji shi

Mark ya gabatar da wasu tsatsare da ya yiwa take da '730' wadanda ya ke ganin za su magance matsalolin Najeriya cikin shekaru biyu. Ya yi alkawarin kawar da talauci, samar da ayyukan yi wanda hakan yasa matasan Najeriya ke jefa rayuwarsu cikin hadari a Teku ko Sahara a yunkurinsu na zuwa kasashen waje domin samun ayyukan yi. Ya kuma ce zai mayar da hankali wjen bayar da tallafi ga masu kananan masana'antu ta hanyar basu bashi mara ruwa saboda su samar da fasahar da za ta bunkasa tattalin arzikin Najeriya da samar da ayyukan yi.



DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA  
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com



No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku