JIHAR BENUE TA SAMU SABON KWAMISHINAN YAN SANDA

- Hukumar yan sandan jihar Benue ta samu sabon kwamishina

- Ya fara aiki ne a ranar Alhamis


- Kwamishinan yayi alkawarin ba mutanen jihar ingantaccen tsaro da kawo karshen ayyukan ta'addanci 



Wani sabon Kwamishinan yan sanda na hukumar jihar Benue, Okon Etim Ene ya fara aiki a hedkwatar rundunar dake Makurdi, babban birnin jihar. Kakakin rundunar yan sandan jihar, DSP. Moses Joel Yamu yace kwamishinan ya fara aiki a ranar Alhamis, 23 ga watan Agusta sannan kuma ya ba mutanen jihar tabbacin jajircewarsa domin yi masu aiki. Sabon kwamishinan ya taba aiki a matsayin mataimakin kwamishin yan sanda dake kula da ayyuka a hukumar ta jihar Benue.

Ya ba mutanen jihar Benue tabbacin samun ingantattun tsaro da magance ayyukan ta’addanci.



Comments