JARUMIN FINA-FINAN HAUSA YA RASU


Allah ya yiwa Ayuba Dahiru da aka fi kira Tandu, jarumi a masana’antar shirya finan-finan Hausa dake Kano, rasuwa.





Da sanyi safiyar yau, Lahadi, ne marigayin ya rasu a garin Kano bayan fama da gajeriyar rashin lafiya kamar yadda dareka a masana’antar Kannywood, Falalu Dorayi, ya shaidawa BBC Hausa.



“Allah ya yiwa Ayuba Tandu rasuwa bayan ya sha fama da zazzabi na kwana biyu. Muna masu addu’ar Allah ya gafarta masa,” in ji Falalu Dorayi.



Kafin rasuwar sa, Tandu ya fi fitowa a fina-finai ko matakin barkwanci. Wasu daga cikin fina-finan day a fito sun hada da Auren Manga da Gobarar Titi da kuma Afrah. Ya rasu ya bar mata uku da kuma yara 9.



Comments