Sunday, August 26, 2018

GWAMNATIN LEGAS TA BUDE GADAR THIRD MAINLAND BRIDGE


Gwamnatin Legas a Najeriya, ta bude babbar gadar da ta sada yankin tsibiri da kan tudun jihar ta kan ruwa, wato Third Mainland, wadda aka rufe ta a daren ranar Alhamis da ta gabata.
A ranar Lahadi, 26 ga Agusta gwamnatin ta Legas ta sanar da cewa da misalin karfe 5 na yammaci za ta bude gadar.
 An dai rufe katafariyar gadar ce, domin gudanar da bincike kan ayyukan sake karfafata da yakamata ayi, gwaje-gwajen da zuwa yanzu, injiniyoyi suka kammala, a cewar babban sakataren ma’aikatar Sufurin jihar ta Legas, Dakta Taiwo Salaam.

 Rufe gadar na gajeren lokaci dai ya haddasa samun cinkoson ababen hawa, a hanyoyin da suka koma bi domin zirga-zirga tsakanin manyan yankunan kan tudu da kuma tsibirin da ke jihar ta Legas.





 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 



No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku