TSIGE SARAKI BA ZAI RAGE FARASHIN SHINKAFA ZUWA N7,000 BA – INJI FAYOSE
Gwamnan jihar Ekiti, Ayodele Fayose, a ranar Laraba yace yana mamakin ko tsige Bukola Saraki a matsayin shugaban majalisar dattawa zai rage farashin buhun shinkafa zuwa N7,000 a kasuwan in Najeriya.
Fayose na martani ne akan kiraye-kiraye da ake yi kan tsige Saraki tun bayan da ya sauya sheka daga jam’iyyar APC mai mulki zuwa PDP. Ya wallafa hakan ne a shafinsa na twitter wato @ayofayose.
A halin da ake ciki, shugaban jam’iyyar APC na
kasa, Adams Oshiomhole ya tirje akan cewa lallai sai shugaban majalisar
dattawa, ya sauka daga matsayinsa ko kuma su tsige shi.
Oshiomhole yace ba zai yiwu Saraki ya yi
jagoranci ba alhalin APC ce ke da mafi rinjayen sanatoci a majalisar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku