DAMUWAR E.U. GAME DA MAMAYAR DA DSS SUKA KAI MAJALISAR TARAYYA
Kungiyar Tarayyar
Turai(EU), ta nuna matsananciyar damuwa dangane da yadda jami’an SSS suka
mamaye Majalisar Tarayya, har kungiyar ta yi gargadin cewa jami’an tsaro su
guji nuna bangaranci wajen amfani da kayan gwamnati.
“Kungiyar ta ce akwai damuwa sosai idan aka buga misali da yadda
ake amfani da jami’an tsaro wajen yi wa dimokradiyya kutse – kamar yadda
jami’an SSS suka kewaye Majalisar Tarayya a ranar 7 Ga Agusta,”.
Haka kungiyar ta EU ta bayyana a cikin wata sanarwar
da ta aiko wa PREMIUM TIMES a yau Alhamis da safe.
“EU ta maida hankalin ta sosai wajen tallafa wa da
goyon bayan tsarin dimokradiyya a Najeriya, kuma ta jinjina wa Gwamnatin
Najeriya dahngane da yadda ta gaggauta daukar matakinn kare dimokradiyya.”
Haka ya ke a rubuce, cikin bayanin da kakakin yada
labaran kungiyar a nan Najeriya, a Abuja.
Haka nan shi ma ofishin jakadancin Birtaniya a
Najeriya, ya yi Allah-wadai da mamayar da SSS suka kai wa Majalisar Tarayya, a
cikin wani jawabi da ofishin ya fitar a ranar Talatar da abin ya faru.
Birtaniya ta ce ba za ta taba amincewa da duk wani
yunkuri na keta haddin dimokradiyya ba.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku