Sunday, August 26, 2018

AN KASHE SHUGABAN KUNGIYAR 'YAN TA'ADDAN ISIS A AFGHANISTAN


- Kasar Amruka ta kashe shugaban kungiyar ISIS na Afghanistan ta hanyar kai hari maboyarsa
- Shi ne shugaban kungiyar ISIS na uku da aka kasha a Afganistan cikin shekaru biyu
- Kasar Amruka ta sha alwashin ci gaba da yaki da kungiyoyin ta’ddanci dake a waje da cikin kasar ta.





Jami’in kasar Amruka ya sanar da cewa, an kashe shugaban kungiyar ‘yan ta’addatan ISIS, wanda yayi shirya tashin wasu bama bamai da suka yi sanadin mutuwar daruruwan mutane a Afghanistan, bayan da Amruka ta kai hari a mabuyarsa.



“Mataimakin mai Magana da yawun shugaban kasar Afghanistan, Ashraf Ghani ne ya sanar da mu mutuwar shugaban kungiyar ta ISIS-K, Abu Sayeed Orakzai”, a cewar jami’in Amrukan, Col. Martin O’Donnell. Cikin wata sanarwa, O’Donnell ya ce: “Haka zalika nima zan kara da cewa, Amruka na ci gaba da yaki da kungiyoyin ‘yan ta’adda kamar su ISIS-K, Al-Qaeda, da dai sauran kungiyoyin ciki da wajen,”



Rahotanni sun bayyana cewa An kai harin ne a yankin Nangarhar, kusa da iyakar kasar Pakistan, inda yai sanadin mutuwar wasu dakarun rundunar ISIS guda 10. Shi dai Orakzai, shi ne kusan shugaban kungiyar ISIS-K na uku da aka kashe a Afghanistan a cikin shekaru biyu. Kungiyar ta ISIS ta rasa iko akan wasu garuruwa da ke da iyaka da kasashen Iraq da Syria tun fara rikicinsu a watan Yulin 2014.

Kisan Orakzai ya biyo bayan wani sakon sautin murya da babban shugaban kungiyar ta IS, Abu Bakr al-Baghdadi ya fitar, inda yake sam barka ga mabiyansa da taya su murnar bukin babbar Sallah Har yanzu ba’a san mabuyar Al-Baghdadi ba tun bayan shaharar kungiyar ta IS. Ya dai taba fitowa fili a shekara ta 2014 a wani gari dake arewacin Iraqi, inda daga bisani akai ta yayata jita jitar mutuwarsa.



 DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
DOMIN TALLA: http://northernstartv.blogspot.com/p/siyasa.html

No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku