YAU MA SHUGABAN KASAR NAMIBIA YA ZIYARCI SHUGABA BUHARI
Bayan karbar bakuncin shugaban kasar Faransa,
Emmanuel Macron, a jiya, yau kuma shugaban kasar Namibia, Hage Geingob, ne ya
ziyarci shugaba Buhari a fadar gwamnatin tarayya dake Abuja.

A hotunan da wani mataimaki na musamman ga shugaba Buhari a bangaren yada labarai, Bashir Ahmad, ya watsa a shafinsa na Tuwita dake dandalin sada zumunta, an ga shugaba Geingob na gaisawa da jami’an gwamnatin Najeriya bayan ya isa fadar shugaba Buhari. Babu wani Karin bayani dangane da dalilin ziyarar ta sa a Najeriya.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta
Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku