SHEKEWAR KWANKWASO ZUWA PDP YA SAUYA LISSAFIN MAJALISAR DATTAWA

Biyo
bayan ficewar wasu gagga gaggan yan siyasan Najeriya dake wakiltar al’ummominsu
daban daban a majalisar wakilan har su goma sha biyar, shugabancin majalisar za
ta canja, kamar yadda ake cewa idan kida ya canza dole rawa ma ya canza.
Sanannen abu ne cewar kafin ficewar yan
majalisun, jam’iyyar APC ce take da rinjaye, inda take da Sanatoci sittin da
hudu-64 yayin da PDP keda Sanatoci Arbain da biyu-42, amma wannan lamari da ya
faru yai sauya lissafin gabaki daya.
Wannan ta sa ba tare da wata wata ba reshe ya
juye da mujiya, inda Sanata Godswil Akpabio daga jam’iyyar PDP, wanda shine
tsohon shugaban marasa rinjaye ya zama shugaban masu rinjaye, yayin da Ahmad Lawan
na APC ya koma mukamin shugaban marasa rinjaye. Sanatocin da suka fice daga APC
zuwa PDP sun hada da Sen. Shaaba, Sen. Melaye, Sen. Shittu , Sen. Rafiu, Sen.
Shehu Sani , Sen. Shitu Ubali, Sen. Isa Misau, Sen. Hunkuyi, Sen. Gemade, Sen.
Danbaba, Sen. Nafada, Sen. Monsurat, Sen. Tejuoso, Sen. Nazif da Sen.
Kwankwaso. Sai dai dayake shugaban majalisa y adage sauran zama har sai zuwa
ranar 25 ga watan Satumba, wannan yasa ba kammala canza sauran mukaman
majalisar ba, amma ana sa ran da zarar an dawo za’a sauya su gaba daya.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku