RA’AYIN SANATA SHEHU SANI GAME DA KUDIN ABACHA

Shehu Sani, Sanata mai wakiltar Kaduna ta tsakiya, bai yarda da shawarar da gwamnatin tarayya ta dauka ba, game da Naira miliyan 320 da aka karbe Abacha. 



Shugaba Muhammadu Buhari ya ce za a sanya kuɗin a cikin asusun jama’a ta wurin (CCT) wanda wa "matalauta 'yan Najeriya".
A ranar Jumma'a, gwamnatin tarayya ta ce za ta fara rabar da kudaden da aka samu kimanin iyali 302,000 a jihohin 19 daga watan Yuli. 
Da yake jawabi game da ci gaba ta hanyar Twitter, Sanata ya ce kudaden zai kare tare da masu amfana "wanda aka ba da sunayensu" ta hannun gwanonin jihohi, sanatoci, ministoci, ‘yan majalisu da kuma magoya bayan shugaba Muhammadu Buhari kawai.
Ya ba da shawarar cewa ‘a mori wadannan kudaden wajen bunkasa tattalin arzikin kasa, ko gudanar da wata aiki ga al’umman Najeriya.
Domin ko wane dan Najeriya ya ci moriyar kudaden da aka kwato daga kasashen ketare.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments