OBASANJO YA BAYYANA WANDA ZAI GOYI BAYAN SA A ZABEN 2019
Tsohon shugaban kasar Najeriya Olusegun
Obasanjo a ranar Alhamis din da ta gabata ya bayyana cewa, wadanda ke lalata
kasar nan ba bu lallai su kasance mamugunta sai dai zababbun shugabanni masu
rike da madafun iko da suka zuba idanu tare da yin shiru kan al'amurran da suka
shafi kasar.
Obasanjo ya bayyana ire-iren wadannan mutane a
matsayin makiya kasar nan ta Najeriya, inda ya sha alwashin ba zai rike bakin
sa yayi shiru yayin da munanan al'amurra ke faruwa, sai dai ya ce a shirye yake
ya goyi bayan duk wanda zai kai kasar nan ga gaci. Dattijon na kasa ya yi
wannan takaddama tare da kaddamar da matsayar sa yayin da tsohon ministan
ayyuka na musamman, Kabiru Tanimu Turaki, ya ziyarci shi a gidan sa dake babban
birnin Abeokuta a jihar Ogun.
Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya
bayyana, Turaki ya kai ziyara ne birnin Abeokuta domin bude sabon shafi tare da
neman amincin da tabarraki na Obasanjo dangane da kudirin sa na neman takarar
kujerar shugaban kasa a zaben 2019.
Obasanjo ya fahimci cewa, kasar Najeriya na da
albarkar amintattun mutane nagari da ka iya jagoranci ko ina a fadin duniya,
inda ya bayyana cewa ba zai gaza ba wajen fafutikar sa ta neman tsayayyen
jagora da zai kai ta ga gaci.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku