MATASHI YA MUTU BAYAN LASHE GASAR SHAN GIYA

Wani mutum dan kasar Kenya mai suna, Mufutu Nyongesa, 25, wanda ya fito daga kauyan Tande, ya mutu a ranar Litinin bayan ya sha giyan da ta fi karfin cikinsa wanda babu komai a cikinsa. 

An ce, Nyongesa, yana shan giyan ne tare da wasu abokaninsa a wata mashaya, sa’ilin da suka yanke shawarar su yi gasan shan giyan. Inda za a baiwa duk wanda ya kwankwadi mafi yawa a kankanin lokaci ladar karin wata kwalbar giya, kamar yanda gidan yada labaran kasar ta Kenya mai suna, ‘Standard Media Kenya, ya bayar da labarin aukuwar lamarin. Bayan da Nyongesa, ya kwankwadi karin kwalabe biyu ne nan take ba kuma tare da kakkautawa ba, duk da cewa cikinsa fayau yake domin bai ci komai ba, sai ya fara jin ciwon ciki. Matar mamacin mai suna, Anne Naliaka, cewa ta yi, mijin nata ya fita daga gida ne domin ya dubo mashin dinsa da ake yi wa gyara a wani wajen gyaran Babura, amma sai ta ga bai dawo ba. 


“Kafin ya fita, ya ce mani na dafa masa Ugali, a matsayin abincin ranan sa, amma sai na ga bai dawo ba. Har rashin dawowar na shi ya bata mani rai, domin na yi zaton ya canza shawara ne, na ya ci abincin a waje. Daga baya ne wani ya kira ni a waya yana shaida mani cewa, ga shi a can yana ta amai, akwai bukatar a hanzarta da shi wajen likita,” in ji Naliaka. Matar, nan da nan ta nemi abokanansa da su kai shi asibiti, amma ko kafin isar su asibitin ma ya mutu a hanya. “Abokaninsa sun shaida mani cewa, ya sha kwalaben giya ne guda biyu, wacce ba a rage mata karfi da ruwa ko Soda ba, sannan kuma ga shi bai ci komai ba,” in ji Matar mamacin. Abokanin sa suka ce, suna jin kakkarfar giyan da ya sha ne tare da yunwa a cikinsa kuma a kankanen lokaci ya yi sanadiyyar mutuwar na shi


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments