KANNYWOOD: JARUMA ZAINAB INDOMIE TA FARKA DOMIN CIGABA DAGA INDA TA TSAYA


Shahararriyar jarumar Kannywood Zainab Abdullahi wacca aka fi sani da Zainab Indomie na shirin dawo da sunanta a masana’antar.
An daina jin duriyar Indomie a masana’antar na tsawon wani lokaci bisa ga wasu dalilai. Ubangidanta Adam Zango ne ya sanar da dawowar jarumar a shafinsa na Instagram. Ya wallafa hotunanta saboda nuna farin cikin sa bisa biyayar da take nuna masa.
Jarumar tana daya daga cikin jarumai mata dake kan gaba da farfajiyar kamfanin White house family wanda Adam Zango ke jagoranta.
Zainab Indomie tana daya daga fitattun matan kannywood da suka raya masana'antar gabanin fitowar sabbin fuskoki da ake damawa dasu yanzu.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments