GWAMNAN BAUCHI YA BA IZALA KYAUTAR FILI DON GINA JAMI’A


wamnan jihar Bauchi, Barista Mohammed A. Abubakar ya yi kira ga Malamai na Nijeriya da su kara zage damtse wurin wayar da kan jama’a dangane da muhimmancin zaman lafiya, da hadin kai a tsakanin ‘yan kasa domin kyautata zaman takewa. Gwamnan ya yi wannan kira ne lokacin da ya karbi bakuncin ‘yan kungiyar Jama’atu Izalatul Bidi’a Wa Ikamatus Sunnah (JIBWIS) a karkashin jagorancin shugaban kungiyar na kasa, Sheikh Abdullahi Bala Lau a gidan Gwamnatin Bauchi a shekan jiya. 

Ziyarar ta Izala dai sun kawo tane domin su jajanta wa Sarkin Bauchi, Gwamnan Bauchi da kuma al’ummar jihar ta Bauchi, a bisa Ibtila’in ambaliyar ruwa da Iska wadda ya yi mummunar wa jama’an jihar mummunar barna, har ma da asarar rayuka, tare da Gobarar da ta lakume miliyoyin naira a kasuwar Azare da ke cikin jihar Bauchi. Da yake bayyana dalilinsu na zuwa Bauchi, shugaban kungiyar Izalar ta kasa, Abdullahi Bala Lau ya bayyana cewar sun kasance a fadar gwamnatin jihar ta Bauchi ne domin su jajanta wa al’ummar jihar akan bala’in da guguwar ta yi, a kwanakin baya, ya yi kuma kira ga wadanda abin ya shafa da su dauki hakan a matsayin wata kaddara ce daga Allah. Bala Lau ya jawo hankulan sarakuna, shugabanin siyasa da masu rike da mukamai da su ji tsoron Allah wajen yi wa jama’arsu aiyukan da suka dace domin haduwa da samun sakamako mai kyau a ranar gobe kiyama. Lau ya yi fatan samun nasarar gudanar da babban zabe 2019 cikin kwanciyar hankali da kuma nasara, inda ya nemi masu ruwa da tsaki da su tabbatar da cewar an gudanar da zaben cikin kwanciyar hankali. Daga bisani kuma ya nemi jama’ar kasar nan da su tabbatar da mallakar katin zabe domin su samu nasarar zaben wadanda suke so a yayin wannan zabubbukan da suke tafe. Wakilinmu ya ruwaito mana wadanda suka mara wa shugaban Izala baya don kai ita wannan ziyarar, sun hada da; Babban sakataren kungiyar ta kasa, Sheikh Kabiru Gombe, shugaban kungiyar JIBWIS reshen Bauchi, shugaban kwamitin ayyuka na kasa Sheikh Abubakar Gero, Daraktan Ilimi na kasa kuma shugaban kungiyar na Kano Dr. Abdullahi Pakistan, Daraktan Agaji na kasa Engr. Mustafa Imam, Mataimakin Daraktan Da’awah Dr. Isma’il Kumo Basirka, Shugaban Majalisar Allarammomi na kasa Abubakar Adam, Sakataren fannin Ilimi Dr. Ibrahim Rijiyar Lemo da kuma Sheikh Khalid Usman. Haka kuma tawagar kungiyar Izalar ta kai irin wannan gaisuwar jajantawar ga Sarkin Bauchi, Alhaji (Dakta) Rilwanu Sulaiman Adamu a fadarsa, inda shugaban JIBWIS ya bayyana cewar sun zo jihar ne domin jajantawa akan wannan masifar da ta auku a kwanakin baya

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com



Comments