FAYOSE YA KAI MA SARAKI ZIYARAR ‘ANA TARE’
Gwamnan jihar Ekiti mai barin gado, Ayodele
Fayoshe ya bayyana ma gwamnatin marasa Imani, biyo bayan farmakin da jami’an
Yansanda suka kai ma shugaban majalisar dattawan Najeriya da mataimakinsa a
gidajensu dake Abuja.
Fayose ya bayyana haka ne a yayin wata ziyara
da ya kai gidan Saraki da Ekweremadu don nuna ana tare a ranar Talata, 24 ga
watan Yuli, inda ya bayyana ziyarar tasa da nufin kara ma Sanatocin biyu kwarin
gwiwa sakamakon tsangwamar da suke fuskanta daga hannun Yansanda.
Daga karshe majiyar NAIJ.com ta ruwaito Fayoshe
ya jinjina ma Sanatoci goma sha biyar da suka sauya sheka daga APC, inda yace
ya sun dade suna tsumayin ficewar Sanatocin daga APC zuwa PDP, inda yace ya
zama wajibi a hada karfi da karfe don fatattakar gwamnatin Buhari.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku