BURIN DANGOTE DAYA DA YA RAGE A DUNIYA NA SAYEN ARSENAL YA KUSA CIKA



- Ansha dai jin yadda Dangoten ke bayyana muradinsa na siyen kungiyar kwallon kafa ta Arsenal
- Wannan dama na daf da samuwa, kasancewar an fara samun baraka a tsakanin masu hannun jari a cikinta




Mutumin da ya fi kowa kudi a Nahiyar Afrika Alhaji Aliko Dangote ya sake bayyana sha'awarsa wajen ganin ya sayi kungiyar kwallon kafa ta Arsenal, hakan ya biyo bayan wasu rahotanni da suke nuni da cewa Alisher Usmanov dan kasar Russia wanda yake da hannun jari har kaso 30% a kungiyar na shirin cire hannunsa daga cikinta.
Wata majiya mafi kusa da Usmanov ta bayyana cewa zai cire hannun jarin nasa ne bisa rashin hadin kai da yake samu daga shugaban kungiyar Stan Kroenke, wajen ganin ya dare kan shugabancin kungiyar. Da aka bukaci jin ta bakin Alhaji Aliko Dangote ya bayyana sha'awarsa wajen ganin ya sayi kungiyar nan da shekaru biyu masu zuwa.
Idan ba a manta ba shahararren mai kudin wanda yafi kowa tarin dukiya a Nahiyar Afrikan ya nuna sha'awarsa a shekara ta 2010 wajen ganin ya sayi kungiyar amma masu ruwa da tsaki na kungiyar suka ki ba shi hadin kai. "Zamu yi kokarin ganin mun sake neman sayan Arsenal a shekara ta 2020 ko da kuwa wani zai saye ta zamu gwada sa'ar mu" Dangote ya bayyanawa manema labarai.

DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments