BUHARI ZAI SHA KASHI HANNUN ATIKU A ZABEN 2019 - PDP ADAMAWA
Shugaban jam'iyyar adawa ta PDP reshen jihar Adamawa, Tahir
Shehu ya bayyana cewa, muddin aka tafi da al'amurra ta hanyar dace to kuwa ko
shakka babbu tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, zai fatattaki
shugaban kasa Muhammadu Buhari daga fadar sa a zaben badi.
A cewar Shehu, tsohon mataimakin shugaban kasar kadai ke da
cikakkiyar cancanta tare da mashahuran makaman yakin da zai sanya ya fatattaki
duk wani dan takara da jam'iyyar APC za ta tsayar a babban zabe na shekara mai
gabatowa. Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, shugaban jam'iyyar
ya bayyana hakan ne a ranar Alhamis din da ta gabata cikin birnin Yola yayin
bayar da sanarwar kaddamar da shirye-shiryen shawagi na yakin neman zabe ga
Atiku da jam'iyyar za ta gudanar a jihar Adamawa. A yayin gabatar da jawabai ga
manema labarai a shelkwatar jam'iyyar ta jihar, Tahiru ya bayyana dawowar Atiku
jam'iyyar ta PDP a matsayin waiwaye da hausawa kan ce adon tafiya ne da ya
kasance babban kamu ga jam'iyyar.
A shekarar da ta gabata ne tsohon Mataimakin shugaban kasar
ya sauya sheka daga jam'iyyar APC zuwa PDP inda a halin yanzu yake fafutikar
neman tikitin takarar jam'iyyar domin lallasa shugaba Buhari a babban zabe mai
gabatowa.
Kazalika Shehu ya kara da cewa, dawowar Wazirin Adamawa
jam'iyyar kadai ya isa ya tabbatar da samun tushen zamanta a jihar Adamawa koda
kuwa ba zai tsaya takarar shugaban kasa ba.
A yayin haka jaridar NAIJ.com ta kuma ruwaito cewa, tsohon
mataimakin shugaban kasar ya bayyana cewa a shirye jam'iyyar sa ta PDP take
wajen tunkarar duk wani kalubale da barazanar tuggu ta jam'iyyar APC.
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku