AYUKAN UNICEF A JIHAR SOKOTO
Babban sakataren ma’aikatar ruwa na jihar Sokoto Hussaini Umar ya bayyana cewa asusun kula da kananan yara na majalisar dinkin duniya (UNICEF) ta gina bandakuna 222 da haka rijiyoyin burtsatse 201 a wasu zababbun kananan hukumomi a jihar.
Umar
ya sanar da haka ne ranar Talata a garin Sokoto a wani zama da gwamnati ta yi
da UNICEF.
Umar
ya ce UNICEF ta gina bandakunan ne domin samar wa mutane da wuraren zagawa da
sukan yi a waje sannan ta haka rijiyoyin burtsatsen ne domin samar da
tsaftataccen ruwa wa mutanen jihar musamman mazauna kananan hukumomi.
Ya
ce rijiyoyin butsatsen da UNICEF ta gina sun hada da na tuka-tuka da wanda ke
amfani da hasken rana sannan asusun na kokarin gyara wasu rijiyoyin burtsatsen
da suka lalace a wasu zabbabun kananan hukumomin jihar.
”
Mun kuma hada guiwa da UNICEF don horar da matasa sana’o’in hannu da inganta
aiyukkan ma’aikatan gwamnati a jihar sannan gwamnati ta samar da Naira miliyan
400 domin ganin an sami nasara kan haka.
Bayan
haka babban sakataren ma’aikatar kiwon lafiya na jihar Mustapha Ali ya ce
gwamnati ta ware Naira miliyan 150 domin samar da magungunan inganta kiwon
lafiyar mutanen dake fama da yunwa a jihar.
”
Sannan mun yi wa kashi 40 bisa 100 na yara kananan allurar rigakafi a jihar
kuma mun dauki matakan da za su taimaka wurin wayar da kan mutane sanin
mahimmancin yi wa ‘ya’yan su rigakafi.”
A
karshe babban sakataren ma’aikatar kasafin kudi na jihar Aminu Dikko da jami’in
UNICEF Muhammadin Pall sun bayyana cewa sun shirya wannan zama ne domin gano da
warware kalubalan da akan yi fama da su a fannonin kiwon lafiya, Ilimi, ruwa,
tsaftace muhalli da sauran su a jihar.
DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/
ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com
Comments
Post a Comment
Ku bada ra'ayoyin ku