ALLAH YAYIWA TSOHON GWAMNAN GOMBE, HASHIDU RASUWA



Allah yayiwa tsohon gwamnan jihar Gombe, Abubakar Hashidu rasuwa.

Wata majiya tace Hashidu ya rasu a safiyar ranar Juma’a, 27 ga watan Yuli a gidansa dake Gombe bayan fama da rashin lafiya na tsawon wasu shekaru. Ya kuma rasu yana da shekaru 74 a duniya. Mista Hashidu ya yi gwamnan jihar Gombe daga watan Mayu 1999 zuwa watan Mayu 2003. An zabe shi a karkashin lemar jam’iyyar All Peoples Party (APP). 

Wani makusancin iyalan marigayin ya tabbatar da mutuwar tsohon gwamnan kuma za’a binne shi da karfe 5pm na yammacin yau Juma’a.


Arigayin ya kuma rike mukamin ministan ruwa da kuma minitan gonad a ci gaban karkara a lokacin mulkin Ibrahim Babangida. 


DOMIN KARIN LABARAI DA KARIN BAYANI KO TAMBAYA, A ZIYARCI SHAFUKAN SADA ZUMUNTA 
FACEBOOK: https://www.facebook.com/northernstartv/  
TWITTER: https://twitter.com/northernstartv  
https://www.linkedin.com/in/northern-star-television-6660bb162/

ZAKU IYA TURO RA'AYOYINKU 'A  nstv@tstvafrica.com KO northernstartv@gmail.com

Comments