Friday, June 29, 2018

KOTU TA KORI KARAR NEMAN TSIGE GWAMNAN JIHAR KEBBI


Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, ta kori karar da aka gabatar a gaban ta, wadda aka kalubalanci sahihancin cancantar Gwamna Abubakar Bagudu zama gwamnan jihar Kebbi.
Bagudu ya samu kalubalanta a matsayin sa na dan takarar gwamna a karkashin APC, daga dan takarar PDP, Sarkin Yaki, wanda ya nemi kotu ta soke satifiket din da aka ba Bagudu, a matsayin wanda ya ci zabe, domin a cewar Sarkin Yaki, bai cancanta ba.
Sarkin Yaki ya zargi Bagudu da kantara wa Hukumar ZABE Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) karya, don haka ya ce ya kamata kotu ta haramta zaben sa da aka yi.
Sai di kuma Mai Shari’a na Babbar Kotun Tarayya a Abuja, Ahmed Mohammed, ya ce mai karar ya kasa gabatar wa kotu kwararan shaidun da za su tabbatar wa kotu cewa Bagudu ya kantara karya.
Dailin haka ne ya kori karar saboda rashin sahihan shaidu.

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com

No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku