Thursday, June 28, 2018

KIRA GA HUKUMOMIN AIKIN HAJJIN NIJERIYA




Dangane da hukuncin wanda aka wuce da shi ta jirgin sama ba a tsaya yin harama a Mikati ba, Shehun ya fada a cikin littafin cewa “Matafiya a cikin jirgin sama, ya fi dacewa su yi harama na Hajji ko Umura a karshen filin jirgin da za su tashi zuwa Jidda tun kafin su zo Mikatin.” Ya dogara ne kuma da fassarar da Sahabban Annabi (SAW), Aliyu bin Abi Dalib (Allah ya girmama fuskarsa) da Abdullahi bin Umar (RA) suka yi wa ayar “ku cika Hajji da Umura don Allah.”, ma’anar cikawar in ji Sahabban ita ce yin harama daga gida ko wurin da mutum zai taso. Ibrahimun Naka’i (RA) ya ruwaito cewa Sahabbai sun so ga wanda bai taba yin Hajji ba idan zai yi Hajjinsa na farko; to ya yi harama tun daga gida. A cikin Ma’alimus Sunani (Sharhi Abi Dawuda), wurin Hadisin Mikati, ya fadi cewa “Ma’anar fadar kafa wurare da Annabi (SAW) ya yi na wadannan Mikati ita ce kar mutum ya tsallaka ba tare da ya yi niyya da harama ba.” Dukkansu sun hadu a bisa cewa idan mutum ya yi harama kafin Mikati, ya isan ma sa (Hajjinsa lafiya kalau), domin ba kamar Mikatin Sallah ba ne da ba a yarda a yi ba sai a lokacin da aka sanya. Har ila yau, a cikin Sharhin Mugni, Dan Kudamata ya ce “Babu sabani kan cewa duk wanda ya yi harama da Hajji ko Umura kafin Mikati, haramarsa ta yi, duk hukuncin harama ya hau kansa.” Ibn Munzul ya ce “dukkan Malamai sun hadu a kan cewa duk wanda ya yi harama kafin Mikati, ya zama mai harama (haramarsa ta yi), sai dai an fi so mutum ya yi a wurin Mikati”. Shi kuwa Buha Isa ya ce “abin da ya fi shi ne alhazai su yi harama tun daga garinsu”. Malamai irin su Alkamatu, Aswadu, Abdulrahman, da Abu Is’haka sun kasance suna yin harama daga gidansu bisa kafa hujja da abin da Uwar Muminai Ummus Salma (RA) ta ruwaito cewa, ta ji Manzon Allah (SAW) yana cewa “Duk wanda ya yi harama da Hajji ko Umura daga Masallacin Baitul Makdisi zuwa Masallacin Allah Mai Alfarma, an gafarta ma sa zunubinsa na abin da ya gabata da wanda ya jinkirta ko kuma Aljanna ta wajaba gare shi.” Abu Dawuda ya ruwaito Hadisin. A lafazin da Ibn Majah ya ruwaito kuma, Hadisin ya ce “Duk wanda ya yi harama da Umura daga Baitul Makdisi ya taho Makka, an gafarta ma sa zunubinsa.” Sayyidina Abdullahi bin Umar (RA) ya yi harama da Hajji tun daga Iyliya’a (Baitul Makdis). Haka nan, Nisa’i da Abu Dawuda sun ruwaito daga Baddi bin Ma’abadi cewa shi (Baddi) ya yi harama daga nan (Baitul Makdis), sai Abdullahi bin Umar (RA) ya ce ma sa “Ka dace da Sunnar Annabinka (SAW)”. Duk wadannan karatuttuka suna bayani ne a kan yin harama kafin zuwa Mikati. Bisa duk wadannan hujjojin da suka gabata, sai Shehu Ibrahim (RA) ya ce, “Tun daga zamanin Sahabbai har zuwa yau, a fili yake cewa yin harama kafin Mikati shi ya fi a kan mutum ya wuce Mikatin ba tare da harama ba.” Mu Nijeriya da sauran wasu kasashen da Mikatinmu ya zo daya, babu filin jirgi a Radinga, don haka kai tsaye ake wucewa Jidda kuma hakan ya sa an keta Mikati ba a yi harama ba. Wasu kasashen, kamar su Misra da Sudan duk za ka ga maniyyatansu sun shiga jirgi da haraminsu. Idan aka zo wurin da Mikati yake, sai a cikin jirgin a sanar da su cewa kowa ya yi niyya. Muma ya kamata a rika yi wa maniyyatanmu haka. Idan kuma direbobin jirgin ba su san Mikatin ba balle su sanar, sai a duba a ga wane filin jirgi ne na karshe wanda idan aka tashi daga shi ba za a sauka a ko ina ba sai Jidda (kamar Khurduum kenan), sai a yi haramar a can. Saboda shi Mikati ba a wuce shi, galibin malamai sun ce duk wanda ya wuce Mikati bai yi harama ba ya wajaba ya yi yanka tare da Istigfari, wasu ma sun ce matukar mutum ya wuce Mikati bai yi harama ba to Hajjinsa sai dai ya bari zuwa shekara mai zuwa ya dawo. Sun fadi haka ne saboda Hadisin Abdullahi bin Umar (RA) da ya ce “Manzon Allah (SAW) ya farlanta Mikati.” Ma’ana tilas ne mutum ya yi harama a nan saboda ya zo da lafazin “Yahillu” watau “Ya yi harama a nan”. Shi labari ne da ya zo da ma’anar horo, inda horo ne ya zo da ma’anar labari sai a ce yana karfafa wajibci ne. Wasu Malamai suka ce idan mutum ya wuce Mikati sai kuma ya sake komawa daga baya ya daura harami a can (Mikatin), shi kenan ba zai ba da jinin nan ba. Wasu kuma suka ce ko da mutum ya koma sai ya ba da jinin. An yarda cewa za a iya yin harama kafin a zo Mikati, amma ba a yarda a wuce Mikati ba tare da an yi harama ba. Wata rana na tambayi wasu manyan malamai uku a Jidda kan cewa mene ne ya sa muke yin harama a Jidda, alhali masana sun san cewa Jidda ba Mikatinmu ba ce? Suka ce gaskiya ne lallai Jidda ba Mikatinmu ba ce, Mikatinmu yana cikin ruwa, sai dai kawai lalura ce take sawa a yi hakan. Amma kuma wasu Malamai sun yi bayanin cewa a batun Mikati babu zancen lalura, domin duk abin da Shari’a ta baiwa mutum kofa a kai, babu zancen lalura. Annabi (SAW) ya ce mutum zai iya daukan haramar Hajji daga can Sham wajen kabarin Annabi Ibrahim (AS), duk kuwa da cewa akwai Mikatin da aka sanya wa mutanen kasar. Bisa fahimtar Malamai, wannan yana nuni da cewa mutum zai iya daukan harama tun daga gidansa. Saboda haka tun da Shari’a ta ba da mafita, bai kamata a rika shige Mikati ba tare da an yi harama ba. Malaman da suka saukaka ne suka ce idan mutum ya yi hakan, dole sai ya yi hadaya, wasu kuma suka ce sai dai mutum ya dawo wata shekarar ya sake yin harama. Don Allah muna kira ga mahukuntanmu na Aikin Hajji su gyara wannan. Domin babu wani Mashahurin Malami da ya taba cewa ya inganta a wuce Mikati ba tare da an yi harama ba. A mako mai zuwa za mu cigaba daga inda muka tsaya cikin yardar Allah (SWT). Wa sallallahu alal fatihil khatimil hadi wa ala alihi hakka kadrihi wa mikdarihil aziym.


Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta

Zaku iya turo mana ra’ayoyin ku a nstv@tstvafrica.com


No comments:

Post a Comment

Ku bada ra'ayoyin ku