BUHARI: KADA KU ZARGE NI GAME DA KISAN GILLAR FILATO




Shugaba Muhammadu Buhari ya  nuna rashin amincewasa don zargin sa da ake yi na na kashe 'yan Najeriya da ake makiyaya a sassa daban-daban na kasar da aikatawa.

Buhari ya yi alwashin kare rayuka da dukiyoyin al’umma da kuma hukunta duk wadanda aka kama da aikata wannan mummunar aika aika.

Bisa ga nasa bayani kuma, Gwamnan jihar Filato ya bayyana cewa sama da rayuka 200 aka hallaka a cikin hare-haren da aka kai a yankunar.

Lalong ya ce hotunan kisan kiyashi da na kare dangi da ake yi wa 'yan jihar marasa laifi, mata da yara suna ci gaba da "azabtar da zukatanmu."

Shugaban ya yi magana a jiya a wani taro tare da masu ruwa da tsaki a garin Jos, babban birnin jihar Filato, bayan kisan da aka yi a wasu al'ummomi a jihar.

Wadanda ake zargi da zaton makiyaya sun shirya kimanin awa 48 a kauyuka takwas na Gashish da Ropp a Barkin Ladi da  karamar hukumar Riyom a jihar Filato suna kasha-kashe.

Ƙauyuka sune Xland, Gindin Akwati, Ruku, Nghar, Kura Falls da Kakuruk duk a yankin Gashish da Rakok, Kok da Razat kauyuka a gidan Ropp.

Yayinda yake mika ta’aziya ga dangin wadanda suka rasa 'yan uwan su, Buhari ya ce kashe-kashen da aka yi a Jihar Zamfara ya fi yawan na Filato, da Benuwe da ma wassu jihohi, inda ya jaddada cewa kada jama’a su dauki kisan da ake yi a Filato a matsayin rikicin addini.
Buhari ya bar Calabar, babban birnin Jihar Cross River, zuwa Jos domin gane wa kansa halin da ake ciki bayan kashe-kashen  ranar Asabar.
Ya ce wadanda suka zarge shi da cewa yaki ya yi Magana da masu kisan gillar wadanda ake zargin Fulani makiyaya ba su yi masa adalci ba.

"Alal misali, halin da ake ciki a Benue.  Dik wani manomi a Benuwe ya san cewa makiyaya a yankin suna amfani ne da sanduna domin kiwo, idan kuma ya zama dole sai su dauki magirbi domin samar wa dabbobin su abinci.

"Amma a yanzu an gaya mini cewa, wadan da suka kai hare-haren suna dauke da AK47, kuma wadansu jama’a suna zargi na da cewa ina goyon bayan masu wannan laifi shi yasa naki in yi masu Magana.
Wannan Magana babu adalci a ciki,

Ya ce: "Zan ci gaba da matsa wa mambobin jami’an tsaro da ke ƙarƙashina domin daukar matakin tsaron rayukan jama’a da dukiyoyinsu.

Comments